(ABNA24.com) Mutane da dama ne suka gudanar da gangami da jerin gwanoa birnin Bagadaza na kasar raki, domin nuna rashin aminewa da katsaladan da kasashen waje suke yi a cikin harkokin kasar.
Wannan dai na zwa e sakamakon yadda wasu suke yin afani da jerin gwanon da ake yi ne kasar wajen tayar da hankali da kuma barnata dukiyoyin gwamnati da na jama’a, da nufin cutar kasar a siyasance.
A nasa bangaren shugaban gungun Hikma Sayyid Ammar Hakim ya bayyana cewa, a halin yanzu babu ko daya daga cikin makusantansa da suke da niyyar tsayawa takarar neman kujerar firayi ministan kasar.
Al’ummar Iraki na zargin wasu masu shiga cikin zanga-zangar da cewa an dauki nauyinsu n daga wasu kasashe domin kawai su kawo tashin hankali da yamutsi a kasar kamar dai yadda ake gani.
/129